
Ashe haka so yake
PAGE 11 * Haka dai nayi ta gurshek’en kuka ba abinda na lasa a baki na ,sai da mama ta kawo mini tea mai kauri na sha San nan ta bani magani nasha zazzabi ne ya rufeni har wajen 4 kamar daga sama naji ana cewa azo akaini dayake ba a bauchin zai zauna ba Aiki ya maido dashi kano,saboda yawan kukan danai idona yayi ja sosai ana fito dani na fara amai bayan an d’aurayen jikina aka sanjan kaya wajen biyar dai-dai aka mika Ni gidana wanda na mai she Shi taskar ajalina ‘yan kai amarya suka kawo Ni suka watse, sai Ni kad’ai kamar mayya ji nake kamar na shigo wata duniyar duk da dakiyar da aka zuban Amma ko kad’an abin bai burgeni ba saboda nasan bada burina zan zauna ba,kulle d’akin nayi yakai na koma kam gado ina kuka. Bayan kamar Rabin awa sai ga muktar da abokan sa,baiyi gigin cewa angwaye a gaida Ni ba don yanda nakeji zuciya ta kamar ta fashe ,Washegari na tashi na fita muktar ya shigo d’akin ya zauna magana yayi min ko kallo bai ishen ba sai ma kuka da nasa ,ina wayyo ma shiga uku Abdulafusace muktar ya jiyo “ke waye Abdul”? nace “Nima ban sani ba”, bai K’ara magana ba ya fita ya ajen leda,kwata -kwata muktar bai burgeni asalima wani haushin sa nakeji,ganin kukan bazai kai min ba yasa na fita ina zaga gidan duk inda na kallah sai naji dama da Abdul ne, flowers nai ta tsinkewa ina kuka ina Yaushe dream d’ina zai zama true,saida duk na b’ata gun San nan na koma nai wanka ko Kwalliya banyi ba don aganina ba amfani, da rana muktar ya dawo duk ya kaasa gane kaina don dayai mini magana saina nahau kuka. Ni meemi na kalli antykhadija nace “tabdi Lalle wan nan soyayya Gaskiya love ko wahala”Anty khadija tace “ke dai bari wata soyayyar kawai jarrabawa ce daga Allah ” nace “to Allah ya sawwake cigaba” Yau satina biyu wanda ya tafi da abubuwa da dama acikin lamura na ciki kwa harda zuciyana data kasaa mantawa da burinta, hakan ya kasancen tamakar jaraba,wanda ya kasance kullum cikin kuka Yau Dana tashi ina karanta Alqur’ani naji wasai azuciyana shine ya bani damar shiga kitchen har na fara girki kawai na k’yale na dawo na zauna ina had’e rai wayata na d’auka na latso wak’ar da Abdul yayimun ina bi hawaye na zuba ,ganin hakan muktar dayake weekend be baije Aiki ba, ya tashi yazo ya d’aga Ni yace “k’anwata wai meya faru dake”?, sunkwi dakai nayi na cigaba da bin wak’ar,wayar ya karb’a ya latsa inda nake dannawa,nan ya d’ago yace “waye Abdul?” bance mai komai ba ,”msg zaki tura mai?”
nan kishi ya murtuke Shi ya dau number d’in yasa awayar sa ,ya shige d’aki, ina zaune tamkar mutum mutumi naji muktar na d’aga murya, jinai yana fad’a da turanci ,tashi nayi na shiga dakin cak ma tsaya , jin yana ambatar sunan Abdul ,dai-dai lokacin ya aje wayar idanuwan sa sunyi jawur gaba nane ya fad’i na suri wayar sa dai -dai lokacin msg ya shigo a wayar na duba naga no din Abdul nai mamamkin yanda akai har ya bugawa Abdul waya ,msg d’in na karanta naga dik na bacin rai ne ,na duba na muktar daya tura mai naga har dasu maganar kai K’ara kotu muktar yace zai kai abdul,kan Abdul ya siye zuciyar matarsa. shima Abdul din bai kasa a gwiwa ba ya fada mai zafa-fa,yana mai cewa tunda aka daura aure bai sake naimana ba ,saboda yasan kimar aure San nan naga yasa har abada bazai manta dani ba kuma,kuka ne na fasa da k’arfi nace “me Abdul yayimah Zakai mai irin wan nan cin zarafi? Amma ka cucen muktar” kan gadon na fad’a ina kuka wiwi da k’arfi naji ya d’ago Ni “meye tsakanin ki dashi ya jijjigani cikin kuka nace “yanzu ya dace ka
gayawa wanda nake ganin mutuncin sa irin haka ,wallahi tamakar Ni kayiwa” ya kalleni yace “ki sani da da yanzu ba d’aya bane yanzu kina k’ark’ashina wallahi ki daina domin d’aukan alhaki wallah Idan ba haka ba ,Yau d’in nan zan gayawa baba” zubewa nayi ina bashi hk’r karya fad’a k’arshen gado na zauna naci gaba da kuka ,muktar yace “inbanda D’an iska tantiri,ace kanaiwa matar aure text” Ni kam nazo iya wuya jinake kamar yana cakan k’aya araina nace “Abdul malami ne bazai haka ba karka manta nice nan nayi mai msg kuma baiyi min reply ba,Nima she’d’an ne ya tunzura Ni da so ,amma kayi hakuri,amma asalima kai ka tsokano shi, Kaine ka bugamai waya kaci mai mutunci ,wallahi akan sa zan baka mamaki” sakatoto ya tsaya yana kallona da alama bana cikin hayyacina ,yace “khadija Anya lafiyar ki Lau? yanzu kika ban hak’uri Amma kuma yanzu kinkuma ce zaki ban mamaki, nifa mijinki ne Amma kike fifita wani akaina ,murmushi nayi nace Abdul shine mijina bakai ba saukar Mari naji a kuncina take na sulale kasa asume.
page 12 * Ashid’e na tashi sabili da ruwan da ya zuban na farfad’o kasa tashi nayi shima muktar sunkuyawa yayi ya d’ago Ni ya rungume yana ban hak’uri kuka nacigaba da rairawa sai Dana tsagaita San nan muktar ya tayardani ya zaunar dani a tsakiyar k’afafuwan sa ,yace “k’anwata ki ganamin mai nene yake faruwa “? nan nace mai “ya muktar bakasan waye Abdul ba ,kayi hak’r da irin maganar da zan fad’a wanda direct daga zuciyana suke fitowa wallahi ina son Abdul so mai tsanani wanda bansan irin son Dana ke mai ba wallahi komi yanda muke da mutum ya zagi Abdul agabana sai na tanka ,Abdul yayi rawargani arayuwata dan wallahi shine nakeso kayi “hak’uri nan na zayyano mai duk farkon soyayyarmu da Abdul” ina dasa aya na fashe da kuka,nace muktar dannamun k’irjina haka yayita dannawa bacci ne ya d’auke Ni ,kamar awa biyu na tashi naga muktar sai Aiki yake haka yazo yace ga abinci na dafa miki naci ba sosai ba.
bayan na gama “yace khadija zangaya miki daga Yau banso ki K’ara ambatar Abdul agidan nan naji mafarin soyayyar ku kuma na tausaya miki sai dai yanzu kin zama tawa babu dalilin da zai sa kina maganar wani,domin ina so na tsare k’imar aure na Niba lusarin namiji bane ,kuma kema ki hankalta domin kina d’aukarwa kanki zunubi,babu ruwan Allah da son da kikema wani kamaki zai da lefi, ah to Idan kunne yaji jiki ya tsira”. Tashi nayi kawai na je d’akina na kwanta ,gabana na fad’uwa domin nasan duk abinda ya fad’a Gaskiya ne ,take na sa kuka ina istigfari, D’an jim nayi kawai kamar me na fara tunanin abdul ,Dana rife Ido sai naga murmushin Abdul kawai jinake Allah ya kawo abin da zai sa auren nan ya rabu, tashi nayi nayi tagumi nan na shiga jerro hailala,ina adduar Allah ya kawon d’auki, bacci ne ya kwasheni akaro na 2 kiran sallar la asar ne ya tada ni,da murmushi akan fuskana na tashi sakamakon wani mafarki danai da Abdul. bayan kwana 2 haka dai nayi ta fama muktar ya d’au zafi dani ko magana baya yi mini Nikam ko ajikina har kar gabana kawai nake ,ko girki mai Dad’i banayi domin Dana fara sai naga ma b’ata lokaci ne ,saboda aganina gwanda na tanadawa Abdul haka muke zaune ba yabo ba fallasa ,wani wa azi na saurara aradio kan matar datakewa mijinta rashin biyayya irin azabar da ake musu ,nan jikina yayi sanyi nasa kuka lokacin na tashi na d’ora girki bayan dawowar muktar yayi mamaki k’warai kuma yaji Dad’inan ,haka na Dirk’usa na naimi gafarar sa ya yafen, ganin hakan yasa yaita rawar jiki sai kawai naji zuciyata na kuna da jin haushin sa, sai shigemin yake Ni kuma ina botsarewa don tukuk’in zuciyata ne ya kuma karuwa sai hararar sa nake kamar ba yanzu na bashi hakuri ba Ni kaina ina mamaki tamkar mai aljanu. kwana biyu ganin na fara sakkowa muna ‘yar mutunci dashi ammamfa zuciyata kullum Tana ga Abdul gashi sai muna bacci naita juyi ina kiran sunan abdul,abin na b’atawa muktar rai ,inaa cikin bacci naji ya d’akan duka nan na tashi na ganshi sai huci yake ,yace “akanme agidana zakina kiran wani”? ko kallo bai isheni ba na koma na kwanta fizgoni yayi na tashi na saka kuka nan jikinsa yayi sanyi ya kamoni yanasan yimin kiss nan na koma da baya Nama fice daga d’akin biyoni yayi yace “haba khadija ya zaki hanani kanki ,bayan kinsan inada hak’k’i akanki ajiyar Yau wata daya Amma kink’i amincemin”! kuka nasa natashi na kuma fita zuciya ta na tuk’uk’i gani nake imde na bashi kaina kamar na rasa wani shashi nane nace Abdul “kai na tanadawa kaina ,Kaine uban ‘ya’yana jikina na bani zan zamo taka”,nan na d’aga hannu sama ina addua Allah ya kawo abinda zai raba auren mu da muktar duk hanyar Dana duba babu dama,b’angaren muktar kuwa duk ya damu ya rame domin ya rasa yanda zai dani ga kishin Abdul na nuk’urk’usar sa domin kullum bakina cikin furta sunan Abdul yake ko kallo muke sai nace ji wani mai kama da Abdul ,sai dai ya kalleni idon sa yayi jajawur. akwai ranar da muktar yasa mana kallon American film Nikam dama ba ma’abociyar kalla bace ranar ne na zauna inayi, kawai aka hasko wasu nawa junan su kiss nan na runtse Ido ina gano kaina da Abdul lumshe Ido nayi ina murmushi ,haka na kwanta na dafe k’irji donji nayi ko ina na jikina yad’au zuuum muktar na kallona ya kashe tv ya daki tebur ya shige d’aki ya fito ya ficewar sa ,nikam bansan me yake bama, dakyar na mike na fita taskar gida ina kallon tauraro da yake lokacin 8:00 kawai jinai kamar k’aran son Abdul ake ga iska na kad’ani zama nayi na hau kuka domin ji nayi duk na sare, saida nayi mai isata na koma gida haka dai mukai ta rayuwa Yau ta kasance wata 2 ina kwance muktar yace zai mini ta dole nan na hau kuka ina karka cucueni haka ya hak’ura,Ni kaina ina mamakin kaina inda ilimina ya tafi sai wataran nayi Abu kuma zan koma nayi ta kuka ina istigfari.
PAGE 13 * “Akwai wata mak’ociyata Tana da yaro guda d’aya sun Saba da muktar saboda akwaishi da son yara sunan sa arif,Yau mamansa ta shigo muka gaisa tace ay mai gidan na yawan bashi alawa tazo godia,muna ta hira da ita sai nake ce Mata yaya sunan sa na Gaskiya sai tace abdul ra’uf sunan su sak da nawa Abdul d’in, nan naji ina k’aunar yaron haka nai ta tulo alawowi, tundaga lokacin yake zuwa duk yamma wataran in weekend ne yana shugowa akwai ranar da ya shigo Ina cewa my Abdullah Welcm na ringumeshi nan muktar ya kalleni ,too anya k’anwata abin naki bai zautaki ba arif ne fa,na kalle Shi nace eh,na sani ai sunan sa d’aya da nawa abdul d’in na gaske Shiisa nake sonsa ,Allah sarki Abdullah na take hawaye ya b’alle sai kuka ,nace ya muktar wallahi ko kare ne,ya nuna k’aunar sa ga abdul zan kaunace Shi ko abinci na dunga bashi ,nan muktar ya yi sakatoto yana girmama soyayyar da nakewa Abdul ,nan yayi dogon naziri ya tashi ya d’au Abdul don mik’ashi gidan su. kwana2 a tsakani muktar ya shirgo uban kaya na k’walama sai washe baki yake ,Nikam ina zaune na rafka tagumi kamar an aiko mini da sakon mutuwa kawai wani tunani na Lula ina tuna wai gai Ni da Abdul muna rayuwa gu d’aya wani murmushi nayi ganin dream d’in nawa yatafi dai-dai,tsaye muktar yayi akaina yana k’aremin kallo tabbas nason yana sona Amma som maso wani yake domin ko ina cike yake taf da dalmar k’aunar Abdul domin ta ruga ta daskare babu wani gu da wani d’a namiji zai samu,wallahi meemi wataran har zama nake taita tunani wai gashi mun rabu da muktar har tununi nayi muktar yayi hatsari ya mutu nayi aure da Abdul ,meemi dakai kalleni a wancen lokacin da sai kin mamakin ramewar danayi Gaskiya so masifa ne. Nan muktar ya tab’ani na d’ago Ido muka had’a Ido nan idona ya kawo ruwa zama yayi ya kamo Ni ya rungume yanabuga bayana,nan na b’arke da kuka ina ya muktar ya zanyi da son Abdul ina tsoron Allah bana son d’aukan zunubi nason inada aure don Allah ka yafen zuciya ta na rasa yanda zanyi nan muktar ya juyoni da salon sa wanda da alama Yau ya samo Shi nan yace sorry wife Nima yanzu na gano yanda kikeji kiyi hak’r Allah shiya tsaramiki hakan bawai don baya sonki ba yak’i baki Abdul ba, Aa sai don nuna ikonsa akanki kuma kinsan matar mutum kabarin sa ,nan ya d’akko min wata leda wan nan sak’o ne inji Abdul yace na kawo miki damm!!kirjina ya bada kida zumbur na mik’e na karb’a na Bud’a alawoyi ne da hisrul Muslim da littafin adduoi ,alawowin n Bud’a na sha nan naji sanyi araina hawaye naji ya kamani har tsikar jikina dake tashi bayan nasha na jiyo na kallo muktar nace “ya ina kasamo”? nan yace “kede anjima zan baki labarin yanda akai,aini yanzu Abdul ya zama abokina Gaskiya yana da kirki” Dad’i ne ya cikan zuciya nan na tashi na tafi kitchen jikina sai rawa yake nan na dawo nace Abdul ,au ya muktar ina dariya nace mai zan dafa ma nan yace Aa nayo take away nan na zauna inaji sai bawa muktar labarin lov nawa da Abdul nake ,idanuwan muktar kam sunyi jawur Amma ya dake don so yake ya sani farin ciki,tare da cimma burin sa.
muna zauna muna hira don yanzu na D’an sake ,shima muktar bashi da aIki sai bani hirar Abdul ta hakan yake samun kaina ,muna zauna sai yake ce dani kin San wanda akai kuwa har Abdul ya bani sako na baki? Nan nace Aa sai ya gyara zama yace “ai ganin yanda duk ki figice komai Abdul sai kace wanda yayi miki asiri da yanda kika d’imauce akansa, harara na kaiwa muktar yayi dariya ya cigaba,nan yasa kishi ke nuk’urk’usa ta har inajin zan iya komai akanki, nan na da nan na shiga binciken sa har Allah yasa na gano she abokin hudu ne abokina shiya gayan ai ya dawo kano d’in ,nan yayi mini kwatancen nida Abdul ke bussness haka na je afusace domin naje ne komai ta fanjama -sanjan,nan Bayan min gaisa naja Shi gefe mukai magana jin nine mijinki kuma duk akanki ne yasa ya bada himma jikinsa har rawa yake yana tambayar yaya kike har da wai Allah yasa ina Kula dake ,zuciya tazo mun wuya naci kwalar sa nan ya ban hkr yasan shine baiyi daidai ba ,zama nai ina Gaya mai ya rabu dake nan ya kalleni yace “ai tunda kukai aure bai sake ganinki ba ,kawai gangar jikin ku ne ba atare ba Amma ruhin ku na tare yayinda yazo nan Azancen sa ,kawai sai na kaimai naushi har yayi hab’o har mutane sun fara taruwa na tarwatsa su ,sai Nazo ina bashi hak’uri,nan dai mukai maslaha har addua yayi mana wallahi khadija yanayi yana hawaye .kallon sa nayi nace sai hakr yakaMata kanemi wata nan abdul ya hararen yace barni kawai yayinda kai min farauta banganin kowce mace da gashi ,kasani aurenku da khadija yasa kaima naji ina k’aunarka saboda ita don girman Allah ka rike ta amana ina rok’anka ka yafe Mata wajen irin yanayin zamantakewar ku,don nasan tunda kazo ka sameni kan maganar nasan da walakin tabbas babu kyau Amma soyayya halittace domin true luv never end,jikinane yayi sanyi nace na d’auki maganar ka Ngd ,Abdul ya fito da leda ahannu yace ka bani izini zanyi kyauta ga matarka, Jim nayi domin daurewa kawai nakeyi saboda kishi ,nan nace ba damuwa haka ya bani yace na kawo miki wallahi khadija har bakin titi ya rakoni man mota na ya k’are haka yaje nan kusa dasu ya sayo bansani ba ya ban na dura ,tabbas Allah shike had’a soyayya na yarda da soyayyrki da Shi Amma ina mai baki hakr ki jure jarabawar da Allah yayi miki har ki fita lafiya ,domin da wuya wallahi k’anwata da wani namijin ne kike mai hakan kina begen wani wallahi da tuni ya miki kaca-kaca wani ma ya sallameki,Amma Ni babu rabuwa a atsakanin mu arazane na dago kai sai na basar ina kukan zuci,azuciyana ina cewa Dama Ni sallamata kayi d’in Dana more,nan naji kaina yayi dim soyayyr Abdul ta ninku araina ga wani tukuki da alhini da nake ji,duhu na gani kawai .sai bud’e Ido nayi na ganni kan ciyar muktar yana min firfita idonsa da alamar hawaye ,yace khadija wallahi ina matukar k’aunarki ,kiyi hkr k’addarar ki ce haka kuka na cigaba da yi yana rungume dani nan na Lula tunanin maganar da ya gayan akan Abdul ,da sauri na d’ago nace muktar yanzu kuna abokantaka dashi? murmushi yayi ya shafa gefen fuskana ,munayi mana ,ai mun zama abokai nan nace naji Dad’i wallahi sosai na dad’a baka girma haka dai rayuwar take tafiya tiryan-tiryan har na cika wata hud’u agidan aurena wanda har alokacin muktar ban bashi hak’k’in sa ba, wanda yake ta farautaa kullu yaumin,wata k’awatace tazo muna hira sai take kallona khadija naga kin K’ara haske Amma kinrame ko dai mun samu ne ,harara na kaimata nace Allah ya sawwke ai Ni.. sai kuma nai shiru ganin zanyi b’aranb’aramar zance, take na Lula tunanin gashi munyi aure da Abdul har min samu babies sai doka murmushi nake,jinai an d’akan duka firgigit na dawo hayyacina karima tace yada tunani haka nan na wayence,da daddare bayan muktar ya dawo ya kawon wasik’a na bud’e tabbas hand writing d’in Abdul ne nan na hau karantawa nasiha ce fall aciki ko ina sayya sa aya da Hadith ya fassara duk akan bin miji nayi biyayya,ahargitse na d’ago na kalli muktar ,nace ya mai kaje kacewa Abdul? nan yace wallahi “bance komai ba asalima munyi wajen 2 weeks bamuyi waya ba,kawai dai ya bada abaki ne yace shine asalin kaunar da zaina cigaba da nuna miki amatsayinki na matar aure ahanzu ,domin yasan za adinga samun matsala to baisan Allah yayi fushi dake shiisa yana nan daram akan malaminki,wani tsagwaron son sa ne ya kuma taso mini take duk na d’auke nasihun Abdul taf akaina kuma nadau damarar Aiki dasu,domin tsoron Allah ya shigeni sosai.
Hakana dage na shiga yiwa muktar biyayya Amma kamar adole nake nasihar Abdul ta shigeni ga kuma adduoin daya rubutomin ,Kullm su nakeyi cikin kwana 2 na samu sa ida zugin ya ragu da radadin,karatu Alkur’ani shine ya Zame min abokin hira ,nan damuwana kashi saba’in ya ragu, Amma natacciyar zuciyata Tana mak’ale da Abdul wallahi meemi scan d’aya bana daina tunanin Abdul,da k’yar da sidin goshi muktar ya Maida Ni cikakkiyar mace aranar nayi kuka na zubda hawaye tabbas Allah shine malikul mulki,lamarin Allah ya wuce musali meemi nayi kokawa da k’addara gashi sai wahala nakesha abanza nan na canja akalar zama na da muktar inamai abinda yakeso Dan tsira rana gobe k’iyama Shi kuma haka yake kyautata mini ,gashi ta gefe suna mutunci da Abdul,kullum nayi sallah sai nayi wa Abdul addua a dukan lamuran sa ,ran nan muna zaune da muktar muna hira sai yake cemuni mai zai sa bazan bawa Abdul k’anwata ko k’awata ba ,damm! naji gabana ya fadi nan kishi wanda bansan ta inda ya fito ba na ji ya shigo ,kuka ne ya fito ,nan nayi sauri na Maida ina istigfari hirar daba a k’arasa ba kenan domin jinai inajin haushin duk yarinyar da Abdul zai aura naji na tsane ta haka na kullo d’aki nayi ta kuka,sai da Abdul yazo ya tambayeni meye nace kaina ke ciwo ban Nuna mai akan maganar da yayi mini ne ba ,sabida nasan baya so,haka ya lallasheni na hak’ura ,haka dai muke zaune cike da kulawa ta bangaren muktar inda yamai dani yar lele Sam baya San b’acin raina ,kome nakeso Shi yake mini,amma azuciyana sai aslow zance domin nikaina nasan bazan daina son Abdul ba gashi kullum sai nayi mafarkin sa.
ina cikin wata na takwas da aure kwatsam Allah ya bani ciki aranar k’aramin suma nayi, kawai gani nake naci amanar Abdul domin nida k’anwar sa muna waya tunda dama k’awata ce haka nai sakin baki na Gaya Mata ina da ciki ,Ni nama manta munyi maganar sai gashi sati d’aya tayi min waya Tana cewa ai kinga Dana Sanar wa da ya Abdul cikin ki dirircewa yayi ya kasa magana wallahi sis hawaye na gani a idon sa nan yace min Allah ya saukeki lfiy ,zai tayaki da addua. ,kunya ce naji ta lullube Ni, na fara hawaye nace “Amma kin cucueni mai sa zaki fad’a bayan kawai ke na gayawa yanzu ya kike so Abdul ya d’aukeni na shiga uku ,nan tasa dariya to meye ai sunna ne kuma Abdul me ilmi ne kinsan ba wanda zai ganki ya kyale to Shi meye nasa aciki ,aranar a suk’uk’u na yini ina ganin kamar naci amanar Abdul ,dariya Anty khadija tayi tace meemi Idan ina Waini abin kamar wadda Banda tunani in Banda abina meye na cin amana ,nan nayi dariya nace “so kenan,Anty khdija cigaba da bani muyi mu gama saboda naga mama nayi min flash” ,dariya Anty khadija tayi tace Okey ruwa ta kurb’a San nan ta ciga haka nai ta rai nan cikin nan muktar duk Shi ke aikin gidan nan, komai ga amai da nakeyi kullum har cikin dare haka muktar zai tashi ya gyara gurun ya gyarani,komai dai shike mini gashi duk abinda nakeso Shi ke mini kyautatawa dai ta gidan duniya na shata agun muktar karkiso kiga yanda nayi kyau baba da mama sai son barka suke, hankalina ya kwanta Amma duk wan.nan bidirin wallahi Abdul na manne araina.
Mama har cemin take ja ira da kika ce ba kyasso Amma ko jibar ki ina Wani rashin so a gareki,?nan nayi murmushi mama ai farin cikinku shine nawa haka tayi ta Shi mini albarka inajin dad’in albarkar da iyayena ke sakamin innaje shike K’ara samun na zauna da muktar ,Amma himm soyayya tana ga Abdul ana cikin hakan watanni suka ja na sauka lafiya na samu baby boy nasha kuka ,meemi saboda tabbas haihuwar ta sanyayamini gwiwa wallahi k’addara ta Riga fata ranar suna muktar yasawa yaron Abdullah ,naji Dad’i sosai nan naji muktar na K’ara girmamashi,Amma fa duk da hakan gani nake wataran zan koma ga Abdul ,sati biyu Abdul yazo ganin takwaransa yana zaune a sitting room ya k’urawa boy Ido yana zuba mai addua kana ganin idanuwan sa kasan daurewa yake kaya ne jibge ya kawo Nikam ina d’aki ina matsar hawaye ,kamar Mara hankali nafara magana yanzu shikenan na rasa Abdul tunda na haihu da muktar haka muktar yazo ya samen,Allah yaso tsohuwar dake Kula dani bata d’akin kuka nasaka sosai ,chaii naji muktar na bani haushi ,magana yake mini nace wallahi ka cucueni Ni ka rabu dani bacci nakeji, jiki a sanyayae ya fita na kullo d’akin ina kuka aranar sai da aka danganani da asibiti saboda zazzabi da damuwa likita yace na rage damuwa yayi min fad’a ,haka muka dawo ina ta kuka ko yaron ban d’auka ba sai da Washegari muktar yace zai gayawa mama, San nan na hak’ura haka dai rayuwa taci gaba da tafiya har nayi arbaa’ina alokacin k’anwar Abdul tazo take gayan ai umman su ta takura sai abdul yayi aure jin hakan yasa naji gabana ya fad’i damm! na nafara in ina idona yayi ja to wace zai aura? nan k’anwar sa tace tab! ai ya Abdul taurin kai gareshi wallahi yace baya son kowa ,ke haka yace bazai aure bama tunda ya rasaki,kuka ne naji ya kubcen nace yanzu maryam mu haka Tamu salon soyayyr yazo zuciyoyin mu ahad’e Amma gangar jiki a ware” ,harara maryam ta bani tace badai kyau takamata yanzu dake dashi kuyi tawakkali saboda dama Allahu bai haliitta zaman ku tare ba ,kuka sosai nayi tayi har kaina ya fara ciwo maryam ma lallashina na hak’ura.
Akawai wata rana nida muktar munje hospital kai Abdul asibiti yana mura,lokacin Abdul yakai umma shima nan muka had’u wallahi gabana fad’uwa yayi tun bayan aurena se yau na kuma ganin Abdul nan da nan na rasa nutsuwa ta haka shima ya fice da sauri kamar zai fad’i Nikam dak’yar nakai kaina kan kujera muna gaisawa da umma,nan umma tayi min nasiha tace. “Rabon wan nan yaron ne ,shiisa kukai ta wahala kai Allah shine sarki sanin gaibu sai Allah ,tabbas Allah shine mai saka so ,na d’auki darasi a rayuwarku keda Abdul domin bawanda bai tsammanin auren ku ba, ubangiji ya Baku zama lafiya da mijinki,aranar ma agida haka na yini asalub’e muktr har ya Saba da yanayina na rashin magana Dana koya.domin tun bayan haihuwata na dad’a yarda na rasa Abdul shine yasa na koyi shiru,soyayyr D’ana kuwa sosai nake mai gashi yaci suna me dadi,haka dai rayuwa tayi ta tafiya Dad’i ba Dadi haka naita fama da so wanda na kirashi cuta asaka har nayi shekara uku da aure wanda acikin hakan na kuma haihuwar baby gal siyama, San nan ga ciwon damuwa danake fama dashi wanda duk dalilin so d’inne.Shakira uku da aurena ummun Abdul ta nuna fushin ta akan Abdul bashiri ta samo mai matar aure Sam baya son matar Amma ba yanda zaiyi haka akai auren shekarar matar daya ta haifi baby gal,take ya saka Mata sunana khadija naji Dad’i sosai alokacin Nima na kuma haihuwa ta uku na samu boy,da kyar da sid’un goshi nake Kula matar Abdul don haushin ta nake ji ,bayanda na iya muke mutunci da ita kuma ganin yanda take Kula da Abdul yasa na sake da ita,Amma meemi kin San wani Abu kuwa wallahi bazan k’arya ba duk kwanan duniya dad’a San Abdul nake kawai na bar abin araina ne, ban san abinda Allah ya b’oye ba ,nan taja numfashi ta tsaya Tare da d’agowa ta kalleni ,tace bari na barki haka meemi ,nan nayi murmushi nace tabbas antykhady kinga soyayya tabbas kyace ASHE HAKA SO YAKE! ,yama fi ga haka sai dai maganinsa hak’uri Gaskiya Anty khadi nayi jimamin labarin ki soyayya ta Gaskiya wadda ba algus tabbas Allah shine sarki mai kashewa da rayawa mai sa so ga wanda yaso alokacin da yaso,tabbas wan nan jarabawace Daga Allah ya jarrabeku yaga imaninku ,Kunyi soyayya Amma duk agareku ba alheri ne ga junan ku ba ke muktar shine alheri gareki ,haka Abdul matar sa itace alheri agareshi domin Allah shine masanin dai-dai,sai dai Allah ya Baku fad’an soyayyr Gaskiya da kukai wa junanku,domin ba zata tafi abanza ba ta Gaskiyace .
PAGE 17 * Anty khadija tayi murmushi tace tabbas meemi kinyi magana mai ratsa jiki naji dadin kasancewa dake,inaso meemi kiban shawara nan na gyara zama nace Anty khadi babu wata soyayya yanzu daya kamata kiyi irin soyayyar Allah da manzon sa ,wan nna soyayya da kika gursa keda Abdul to ki Maida ta ga annabi ,yazamo shi kikewa irin wan nan soyayyr ,to wallahi kin gama dacewa domin son manzon Allah shine soyayya Mara yankewa zaki samu shiga gun Allah da manzon sa duniya da lahira,yanzu duk fadin duniya nan babu wanda zaki mai irin soyayyr nan sai manzon Allah S.W.A a domin shiya cancanta,kuma ba a had’a soyayyr sa da wani, salati agareshi da bin abinda yayi hani da wanda ya umarta shine,kanki fita hayyacin ki aka soyayya face soyayya Allah da manzon sa.Aunty khadi da hawaye ya kwaranyo mata tace tabbas maganar ki itace dai-dai Allah yayi mana mai kyau nace Amin.nan Anty khadi ta kuma kallona tace meemi San nan kinsan me wallahi jiya sai da nayi mafarki gani nida Abdul muna zaune muna hira awani guri munata dariya tunda na tashi nakejin sabuwar soyayyar sa ,inaa so ki fad’awa makaranta su tayani da addua domin shine mak’sudin ma dayasa na bada labarina saboda nasamu wasu su tayani da addua domin kullum abin sabo fill yake dawo min nasan zasu ce son zuciya yasa Aa kullum cikin adduar Allah ya ciremin nake yasamun soyayyr mijina, wallah nikaina narasa yanda nazan nan ta sunkuya tana kuka ,tashi nayi na dafa ta nace Anty kiyi hkr komai Daga
Allah ne tayiwu wan nan itace jarrabawar da Allah ya saka miki ,kiyi k’ok’ari ki cinyeta, kiyi amfani da shawarar da na baki,ki yawaita salati da istigfari da karatun Alkur ani duk da nasan kinayi,Amma ki dage da kinji abin ya bijiro miki ki hau tasbihi insha Allahu komai zai zama tarihi, rungume Ni Anty khadi tayi tana min gidiya tace meemi nagode da kika bani lokacinki tabbas marubuta muna godia nagode nan nayi murmushi nace bakomi Allah Nima nagode haka na tashi nayi sallar azahar ina idarwa Kiran mama na kuma shigowa nan na mik’e nayiwa Anty khadi sallama ta rikeni ta mik’on leda, nace tabdi wallahi bazan karb’a ba dariya tasa tace kin ma isa ,Ni fa yanzu kina matsayin k’anwata, Amma na baki Abu kice bazaki karb’a ba ,fita nayi ya biyoni tace inma baki karb’a ba zan bayar a kawo miki nace Nikam banaso Dan kawai na rubuta labarinki sai kin ban wani abun ,Nikam nayi don Allah da annabi ne ,fita nayi muka d’agowa Juna hannu *tammat bihamdillah*makaranta anan na kawo wan nan tak’aitaccen labarin wanda ya kasance Gaskiya ne ya kuma kunshi darussa da dama da fatan darussan dake cike kun d’auke Shi San nan Antykadija na barar adduar ku Nima meemi nace ku tayata da addua fans D’ina basai na kumai muku sharhi akan wan nan book ba domin ku da kanki nasan kun fahimci abinda sak’on ya aika.
Leave a Reply